Jahar Sokoto

Hausa

Shirye shirye na cigaba da kankama domin tabbatar da ganin shirin noman shinkafa dake gudana a karkashin shirin bayar da ramce ga manoma na babban bankin kasa CBN, a Jahar Sokoto ya samu nasara.

Photo Type: 

Kwamitin da Gwamnatin Jahar Sakkwato ta kafa domin tantance yawan yan asalin Jahar dasuka cancanci samun kudin tallafin karatu, ya samu nasara gano dalibbai 706 na bugi, abinda yasa akasamu tsira da naira miliyan 30 na kudin Jahar.

Photo Type: 

An kalubalanci Sarakunan gargajiya da shuwagabannin addini dasu shige gaba wajen wayar da kan al’ummarsu akan bukatar da ke akwai na karbar shirin tsarin tazarar iyali, domin samar da al’umma ta gari mai cikakkar lafiya.

Photo Type: 

An samu Karin masu cutar amo sanin jini da kashi goma sha daya, shekarar bara a Jahar sokoto.

Babban jami’in kungiyar jakadun masu yaki da cutar amosanin jini Dr. Auwal Ahmad ya sanar da hakan, ya yin da yake gabatar da wata kasida a dakin taro na Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto.

Photo Type: 

Kimanin jekadun kiyon Lafiya tamanin ne aka baiwa horo domin wayarda kan jama’a akan illololin curutoci dabam dabam a saqo da lungu dake jihar nan.

Wannan ko an fito da shine a yayin bukin ranar cutar sikila ta duniya da aka gudanar a dakin taro na asibitin kwararru ta sakkato.

Photo Type: 

Manyan dilolin Startimes dake jihar nan da suka shiga takarar cin garabasar da kamfanin yayi na wannan shekarar an basu na’urar talabijin kirar startimes mai girman inci 32.

wadannda suka samu nasara sune kamfanin Aljabal Digital Concept da kuma kamfanin  NAS Alkali.

Photo Type: 

kungiyar yan jaridu mata takasa reshen jahar sokoto tayi kira ga iyaye musamman masu hali da yan kasuwa kada suyi kasa aguiwa wajen cigaban kansu da samarda kudi domin cigaban diyansu.

Photo Type: 

An karrama ma’aikata ukku na makaran tar tunawa da sarkin musulmi Abubakar na ukku akan dagewar su ga aiki.

Photo Type: 

Gwamnatin jihar sakkwato tayi watsi da jita jitar da ake yadawa a jihar nan cewar ta kwace dukkanin ayukkan majalisun kananan hukumomi ban da albashi. 

Photo Type: 

Masu hulda da kamfanin Dangote kimanin dari da hamsin ne daga jihohin sokoto Kebbi da kuma  Zamfara ne suka ci kyaututtuka a yayin wata garabasa da kamfanin yayi na yan kwanakkin nan.

Photo Type: