Jahar Sokoto

Hausa

An zabi sabbin shuwagabannin da zasu tafiyarda kungiyar iyayen yara da malammai ta kwaleji gwamnatin taraiya dake nan sakkwato.

Zaben da aka gudanar a harabar makarantar ya samu sanya idon wakilai daga  ma’aikatar ilmi ta kasa mrs Edith O. Osanyipefu, da  Malam Hamisu Ali Kofar Mata.

Photo Type: 

biyowa bayan karewar wa’adin shugabancin ta shugabar majalisar  kungiyoyin  mata ta kasa reshen jihar sakkwato A’ishatu utiya ta sauka daga wannan matsayin.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani bayani da shugabar mai barin gado ta fitar da kuma ta aikewa da sashen labarai na vision.

Photo Type: 

Gwamnatin jahar sakkwato na shirin kafa sababbin kamfuna na sarrafa tumatur da na takin zamani da kuma na sumunti.

Gwamnan jaha aminu Waziri Tambuwal ne ya fadi haka  a rana ta musamman ta jahar sakkwato a kasuwar bajakoli karo na talatin da takwas  da akayi a jahar Kaduna.

Photo Type: 

Anbukaci jama’ar dake zaune ashiyyar gandu da kenan babban Birnin jaha dasu rungumi dabi’ar tsaftar muhalli tare da hadakai ga shiraruwa da manufofin gwamnati kan suzama afadake akan ayukkan da gwamnati ta samar a shiyyar.

Photo Type: 

Bisa ga amincewa da shawarar mai martaba Sarkin musulmi Alhaji muhammad Sa’ad Abubakar na ukku, gwamnan jahar Sokoto  Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da nada Alhaji Muhammad Tukur Ambarura a matsayin sabon uban kasar Ambarura.

Photo Type: 

Aikin shimfida titin  Shehu kamba dake shiyar Gidan Haki a nan cikin garin Sokoto da hukumar tsara Birnin sakkwato da kewaye keyi yakai wani mataki na kammalawa.

Director General na hukumar  Sani Daudu Yabo ne ya bayyana haka yayin da yake magantawa akan wannan aikin.

Photo Type: 

Jami’an da ke kulada aikin tantance kayyaki daga hukumar kwastam sunyi bayanin cewa zasuyi iyakacin kokarinsu domin tabbatar da an baiwa dukkanin masu motocin da hukumar ta kwace motocinsu bayan biyan kudin duty.

Photo Type: 

Daga yanzu ba zaa sake lamunta da dabiar nan ta azo ofis a saka hannu a rajista a wuce ba a wannan zamani na mulkin gwamna aminu Waziri Tambuwal,

Photo Type: 

Anyi kira ga al’umman musulmi dasu soma duban jinjirin  watan jumada sani 1438 bayan hijira, daga gobe litinin, 27 ga watan febrairun 2017,wanda zai zama 29 ga watan jumada auwal 1438 bayan hijira.

Photo Type: 

Gwamnatin jahar sakkwato ta soma wani hadin gwiwa da masu sanya jari daga kasar Turkiyya domin farfado da masana’antar kera kujeru da gadaje ta jahar sakkwato.

Photo Type: