Jahar Sokoto

Hausa

Kungiyar yan jarida reshen jahar nan tare da hadin gwiwa da ma’aikatar lafiya ta jahar sakkwato, sun shirya ganawar keke-da keke da shuwagabannin al’ummar shiyar gandu dake nan birnin sakkwato.

Photo Type: 

Hukumar  kula da gidajen yarin najeriy ta fitar da takardar kara ma ma’aikata dubu goma da dari tara da saba’in da tara girma daga sassan garuruwa acikin kasar nan

Photo Type: 

Gobnor Aminu Waziri Tambuwal  yayin kira ga wadanda suka amfana da shirin karfafa gwiwa na inganta noma da cigaban karkara na kasa da suyi amfani da kayan aikin da aka basu ta yadda ya kamata 

Photo Type: 

Gwamnatin jahar sokoto zata karbi bakuncin gasar karatun kur’ani maigirma ta makarantun da bana arabiyyaba wanda za’ayi nan sakkwato.

Photo Type: 

Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya ya shirya wani taro na wuni biyu da shugabannin kafafen yada labarai na jahohi uku na arewa maso yamma don yin bita akan rawar da kafafen yada labarai ke takawa gameda kula da lafiyar iyaye da kananan yara , 

Photo Type: 

An bayyana karin farashin man fetur dakuma kasawa wajen samar da isasshen Abinci a matsayin ababen da ke haddasar da tashin farashin abinci da kayan masarufi a najeriya.

Photo Type: 

An lura da cewa mummunar dabi’ar nan ta karancin mai ta sake dawowa a birnin sakkwato tun kwanaki biyu da suka wuce.

Wakillan mu wadanda suka zagaya acikin gari sun bamu rahoton  cewa mafi yawan gidajen Mai suna nan a rufe.

Sunce yan’black market suna sayar da man ne a matsanancin farashi.

Photo Type: 

An lura da cewar mafi yawanci makabartun dake jihar nan na cikin yanayin maras kyau.
Wannan dai na daga cikin ra’ayoyin jama’a da suka bayar da gudummuwa a shirin Sakkwatawa kwallahiya da wannan Gidan rediyo na Vision ya gabatar yau yayin da suke tsokaci akan muhimmancin kulawa da makabartu.

Photo Type: 

Makarantar Adiyya Islamiyya dake shiyar sabon birni a nan cikin garin Sokoto ta yaye dalibbai Arba’in da takwas.
Dalibban da aka yaye sun hada da maza goma sha shidda da mata talatin da shidda.

Photo Type: 

Shirin kawar da zaizayar kasa da kula da magudanun ruwa na ma’aikatar muhalli ta kasa tare da hadin gwuiwar Babban bankin Duniya sun shirya wani taro na wuni daya ga yankunan da abin ya shafa.

Photo Type: