Jahar Sokoto

Hausa

Shugaban kwamitin zakka da wakafi na jihar nan Malam Lawal Maidoki, yace fiye da naira miliyan 6. Ne aka kashe wajen yin magani ga masu matsalar tabin hankali su 965 a jihar nan.

Photo Type: 

Gwamnatin jahar Sokoto tare da hadin guiwar bankin duniya karkashin maaikatar muhalli ta fito da wani shiri mai taken shirin kula zaizayar kasa da albarkatun ruwa a najeriya, wato NEWMAP

Photo Type: 

Anyi yi kira yan kasuwa a jahar Sokoto da su zunduma a cikin harkar noma don marawa gwamanatin jahar Sokoto baya a kokarinta na samadda ayukkan yi ga jamaa, da kuma kawadda fatara hadi da sammadda isasshen abinci a jahar nan.

Photo Type: 

Gwamnatin jihar sakkwato tace ta ware fiye da naira biliyan 13 a kasafin kudin bana a haujen aikin gona.
Governor Aminu waziru Tambuwal ne ya baiyana haka yayin kaddamarda shirin noman shinkafa na Dangote a wurin shirin noman Rani dake Goronyo.

Photo Type: 

A zaman Wani bangare na tabbatar da ganin cewa dokar tabaci da gwamnatin Jihar Sokoto ta kaddamar a akan sha’anin Ilimi ya samu nasara, Kwamitinanan Ma’aikatar ilimi mai zurfi Alhaji sahabi Isah Gada, ya ziyarci kwalejin kimaya da fasaha ta Ummaru Ali Shinkafi da kwalejin nazarin ayukkan shari’a da addinin musulunci

Photo Type: 

An yi kira ga masu rike da mukaman siyasa dasu kasance wakillai na gari ga jama’ar da suka zabe su.

Photo Type: 

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanya hannu ga kasafin kudin shekarar 2017 na fiye da naira biliyan N204.3 billion.
Da yake jawabi gwamna Aminu Tambuwal ya nuna jin dadin sa akan yadda majalisar dokoki ta jiha ta gaggauta kammala aikin kasafin kudin.

Photo Type: 

Ta bayyana jindadin ta akan kyakkyawar kulawar da gwamnatin jaha ke baiwa baiwa fannin aikin noma a jahar nan, musamman noman shinkafa, alkama da kuma tumatur. Shugaban kungiyar na jaha Alhaji Haruna Abubakar bayyana haka a cikin wani bayani.

Photo Type: 

Hukumar hana fasa kwabri mai kula da Jihohin Sokoto, da Kebbi da kuma Zamfara ta tara sama da Naira Biliyan 294 kwatankwacin kashi 122 na kudin shiga a shekara ta 2016. Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Musa Adamu Yusuf ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka raba ta ga manema labaru.

Photo Type: 

A kokarin da yake yi domin yaki da cutar malaria Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da kafa hukumar da aka baiwa alhakin yaki da cutar.

Za’a rinka kiran hukumar, Hukumar yaki da cutar malaria ta jihar Sokoto.

Photo Type: