Gwamnatin Taraiya

Hausa

Uwar Gidan shugaban kasa Aisha Buhari, tayi kira ga matan gwamnoni da su bayar da fifiko wajen karfafawa mata da kuma matasa a matsayin wata hanya da zata kawarda  kwankwadar miyagun kwayoyi a Arewacin kasar nan.

Photo Type: 

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi kira ga ma’aikatan gwamnati a kasar nan da suyi amfani da ayukkan su wajen yima kasar nan hidima.

Osinbajo ya bayar da wannan shawarar ne yayin bude laccar rubu’in shekara na farkon akan sha’anin aikin gwamnati a Abuja.

Photo Type: 

shugaban kwamitin majalisar dattawa dake kula da albarkatun mai  Donald Alasowadura, ya tabbatar da cewar za’a amince da dokar da ta shafi albarkatun mai a cikin wannan watan na maris.

Photo Type: 

Mataimakiyar babban sakataren majalisar dunkin duniya  Amina Mohammed, tace akwai  bukatar fitowa da wasu dubaru domin kulawa da jama’ar da yanzu haka  ke fuskantar matsaloli dabam dabam a Arewa maso gabascin Nijeriya.

Photo Type: 

Gwamnatin taraiya ta bada amannar cewar za’a kara samun hako danyen mai a kasar nan.

Manajan daraktan babban kamfanin mai na kasa NNPC, Dr Maikanti Baru, ne ya baiyana haka a cikin wani jawabi da ya gabatar a wurin babban taron sha’anin Mai da iskar Gas karo na goma  16‎.

Photo Type: 

Ministan Makamashi, ayukka da gidaje  Babatunde Fashola, ya kaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna da ta ci kudi naira biliyan daya da miliyan dari daya.

Photo Type: 

Babban sifetan yan sanda na kasa  Ibrahim Idris ya umurci daukacin kwamishinonin yan sanda a kasar nan da a ko yaushe su tabbatar da sun rin ka binciken manyan laifukka har i zuwa karshen su .

Photo Type: 

Kasashen rasha da kuma  China sun hau kujerar naki akan matsayar da majalisar dunkin duniya ya dauka na kakabawa kasar siriya takunkumi akan zarginta da yin amfani da makamai masu guba,

Wanda wannan shine karo na 7 da Rasha ke fatali da matakin na majalisar dunkin duniya domin goyon bayan kasar siriya.

Photo Type: 

Majalisar wakillai ta kasa ta lashi takobin hukunta duk wata asibiti da aka kama cikin zargin yin almuzarranci da da kudi naira biliyan 350. da aka samar domin kaddamarda shirin inshorar kiyon lafiya na kasa watau NHIS.

Photo Type: 

Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harakaokin siyaysa na musamman babafemi ojudu ya caccaki sarkakiyarda ake yadawa a kafaifan sada zumunta na zamani tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Photo Type: